Falalar Azumin Wataran Ramadan
RAMADAN KAREEM!!!
Ramadan Mai Yawan Albarka
MA’ANAR AZUMI MA’ANAR azumi a yaren Larabci, shi ne kamewa daga barin ko mene ne, kuma akan yi amfani da kalmar a kan kowane irin kamewa, kamar yadda (SWT) ke bada labari a kan Maryam (AS), inda take cewa, lallai ni na yi alwashi ga Allah mai rahama zan yi azumi (Suratul Maryam 26).
MA’ANAR AZUMI MA’ANAR azumi a yaren Larabci, shi ne kamewa daga barin ko mene ne, kuma akan yi amfani da kalmar a kan kowane irin kamewa, kamar yadda (SWT) ke bada labari a kan Maryam (AS), inda take cewa, lallai ni na yi alwashi ga Allah mai rahama zan yi azumi (Suratul Maryam 26).
Ma’anar azumi a shari’a, shi ne kamewa daga abubuwan da suke sanya cin abinci ko karya azumi daga bullowar alfijir zuwa fa]uwar rana tare da niyyar bautar Allah mai girma da ]aukaka.
Azumi yana daga cikin mafi girman da’a da kusaci da Allah mai tsarki, kuma Allah Yana bada lada wanda ba shi da iyaka ga mai yin shi, da shi (azumi) ake yin gafarar zunuban da suka gabata, kuma Allah Yake nisanta fuskar mai yin shi daga barin wuta, kuma yake cancantar da shigar shi aljanna.
FALALAR AZUMI DA FA’IDOJINSA
FALALAR AZUMI DA FA’IDOJINSA
1. An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, Allah mai girma da daukaka ya ce, dukkan ayyukan ]an Adam nasa ne, amma ban da azumi, domin azumi nawa ne, kuma ni ne zan yi sakayya domin azumi garkuwa ne, duk ranar da mutum yake yin azumi baya zina, baya daga murya, kuma ba ya yin wauta don idan wani ya zage shi, ko ya neme shi da fa]a lallai ya ce, ni ina yin azumi (sau biyu) Manzon Allah (SAW) ya ce, na rantse da wanda raina yake hannunsa, warin bakin mai azumi ya fi kamshi a wajen Allah ranar kiyama daga kamshin turaren Almiski, kuma mai azumi yana da farin ciki guda biyu da zai yi farin ciki da su, lokacin da yake yin buda baki, zai yi farin ciki da lokacin da zai hadu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa. (Bukhari ya ruwaito hadisi na 1904 da Muslim Hadisi 1151).
2. An karbo daga Sa’ad dan Sa’ad (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, lallai a cikin aljanna akwai kofofi guda biyu ana kiransu da suna Arrayyan, babu wanda zai shige su sai mai azumi, babu wani wanda zai shige su sai su (wato masu azumi). Za a ce ina masu azumi? Sai su mike, sai a ce babu wanda zai shige ta wanda basu ba, idan suka shiga sai a rufe kofar aljannar. Ba mai shiga wannan }ofa ta Arrayyan sai masu azumi, (Bukhari ya ruwaito hadisi na 1896 da Muslim Hadisi 1152).
3. An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, duk wanda ya azumci watan Ramadana yana mai imani, yana mai neman lada, to, an gafarta masa zunubansa wanda ya gabatar (Bukhari ya ruwaito hadisi 1900 da Muslim 760).
AZUMI YA KASU KASHI BIYU
* Akwai azumi na wajibi (dole ke nan).
* Akwai azumi na nafila.
Azumi na wajibi wanda yake dole shi ma ya rabu kashi uku.
* Akwai wanda yin shi dole ne, a wani lokaci ayyananne, shi ne watan Ramadana.
* Akwai wanda yake dole ne saboda wani (illa), wato dalili wanda yake wajabta, kamar kaffarar zihari, ko na kisan kai a kan kuskure, ko na rantsuwa da sauransu.
* Akwai wanda yake wajibi ne mutum ya lizimta wa kansa yin azumi (kamar alwashi).
* Akwai azumi na wajibi (dole ke nan).
* Akwai azumi na nafila.
Azumi na wajibi wanda yake dole shi ma ya rabu kashi uku.
* Akwai wanda yin shi dole ne, a wani lokaci ayyananne, shi ne watan Ramadana.
* Akwai wanda yake dole ne saboda wani (illa), wato dalili wanda yake wajabta, kamar kaffarar zihari, ko na kisan kai a kan kuskure, ko na rantsuwa da sauransu.
* Akwai wanda yake wajibi ne mutum ya lizimta wa kansa yin azumi (kamar alwashi).
AZUMIN WATAN RAMADANA
Hukuncin yin azumin watan Ramadana wajibi ne kowane Musulmi baligi, mai hankali lafiyayye mazaunin gida, kuma rukuni ne daga rukunen Musulunci, littafin Allah (Alkur’ani) da sunna sun tabbatar da haka, har da ijima’in malamai.
Hukuncin yin azumin watan Ramadana wajibi ne kowane Musulmi baligi, mai hankali lafiyayye mazaunin gida, kuma rukuni ne daga rukunen Musulunci, littafin Allah (Alkur’ani) da sunna sun tabbatar da haka, har da ijima’in malamai.
Allah mai girma da ]aukaka ya ce, ya ku wa]anda suka yi imani, an wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta wa wa]anda suka gabaceku ko kwa ji tsoron Allah. (Suratul Bakara 2 aya ta 183).
Manzon Allah (SAW) ya ce, an gina Musulunci a kan abubuwa guda biyar, Shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu (SAW), Manzon Allah ne da tsayar da Sallah da bayar da Zakkah da kuma aikin Hajji da Azumtar watan Ramadana. (Bukhari ya ruwaito shi Hadisi na 8, da Muslim Hadisi na 16 daga Abdullahi ]an Umar, Allah Ya yarda da shi).
Wani Balaraben }kauye ya zo wajen Manzon Allah (SAW) kanshi a cukurku]e, ya ce, ya Manzon Allah (SAW) bani labarin abin da Allah ya farlanta a kaina na azumi, sai Manzon Allah (SAW) ya ce azumin watan Ramadan, sai dai kuma in ka so ka yi azumin nafila (Bukhari ya ruwaito shi Hadisin na 50 da Muslim Hadisi na 9, daga dalhatu ]an Abdullahi, Allah Ya yarda da shi).
Lallai Ha}i}a malaman Musulunci sun yi ijima’i a kan cewa, azumi rukuni ne daga cikin rukunen Musulunci, sanannu a cikin addini, to, inda suka ce ana iya kafirta wanda duk ya yi musun azumtar watan Ramadan, kuma azumin baya fa]uwa a kan kowane balagagge mai hankali, sai dai da wani uzuri daga uzurorin shari’a, wacce take abin lura (Al-Ifsah na Ibnu Hubaira) Mujalladi na 1 shafi na 232 da Al-Mugny na Ibnu {uddama, mujalladi na 3 shafi na 285 da Al-Majmu’u na Imamun-Nawawi, mujalladi na 6 shafi na 252).
FALALAR WATAN RAMADANA DA YIN AIKI A CIKIN WATAN
An karbo daga Abu-Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, idan watan Ramadana ya shigo, ana bude kofofin sammai, kuma ana rufe kofofin wuta, ana kuma daure Shaidanu (Bukhari ya ruwaito shi Hadisi na 1899 da Muslim Hadisi na 1079).
An karbo daga Abu-Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, idan watan Ramadana ya shigo, ana bude kofofin sammai, kuma ana rufe kofofin wuta, ana kuma daure Shaidanu (Bukhari ya ruwaito shi Hadisi na 1899 da Muslim Hadisi na 1079).
Daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, salloli biyar, daga Juma’a zuwa Juma’a, da kuma Ramadana zuwa Ramadana, suna kankare abin da ke tsakaninsu, idan sun nisanci manyan zunubai. (Muslim ya ruwaito shi Hadisi na 233).Daga Abu-Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, dukkan ayyukan dan Adam na shi ne sai dai azumi nawa ne. Kuma ni zan yi sakayya da shi (Bukhari ya ruwaito shi Hadisi na 1904 da Muslim Hadisi na 1151)
Babban Malami Abu Amr Ibnu Abdulbarri Almaliyy (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, fadin Manzon Allah (SAW) azumi nawa ne ni zan yi sakayya da shi ya ce, wannan ya isa falala ga azumi a kan sauran ibadoji, sai dai ya ce malamai sun yi sabani a kan abin da Allah (SWT), yake nufi da azumi nawa ne, ni zan yi sakayya da shi tare da cewa, kowane aiki nashi ne (wato Allah SWT), kuma shi ne yake yin sakayya da shi, sun yi sa~ani mai yawa (wato manyan malamai) na farko, sun ce domin azumin riya ba ta shiga cikinsa, kamar yadda yake a cikin ayyuka. Imamul kurdubi (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, da yake ayyukan riya tana shiga cikinsu, to, amma azumi babu riya a cikinsu. Domin shi aikin ana yin shi ne tsantsar shi ga Allah (SWT) shi ya sa Allah Ya jinginashi zuwa gareshi (wato shi ne ya ce azumi nawa ne, ni ne zan yi sakayya da shi) (daga Asarabul Muhibbina Fi Ramadan na Muhammad Hussaini Yakub shafi na 18).
* Alhafiz Ibn Rajab Alhambali (Allah Ya yi masa rahama), ya ce malamai sun yawaita maganganu a kan ma’anar fadin Manzo (SWA), inda ya ce Allah (SWT) ya ce azumi nawa ne zan yi sakayya da shi.
Ya ce, malamai sun ce, lallai azumi shi ne barin raba zuciya da sha’awoyinta na asali, wacce Allah Ya dabi’anceta a kan karkata zuwa ga Allah (SWA) ya ce, ba a samun wannan a sauran ibadoji sai dai azumi kawai.
* Na biyu suka ce, lallai azumi sirri ne tsakanin bawa da Allah (SWA) babu wata ibada da ke da wannan, kuma niyya ce ta boye, kuma ba mai iya tsinkayar wannan sai Allah, kuma ya bar sha’awarsa wacce a]abi’ance na al’ada, shi ya sa babu riya a cikinsa ta inda mutum yana barin abin da zuciyarsa take kiransa zuwa gareshi na son sha’awa babu wanda ke iya tsinkayar wannan sai Allah (La]a’iful Ma’arif Na Ibnu Rajab Alhambali shafi na 209-212).
Allah ya taimake mu.
Comments
Post a Comment