Azumin Watan Ramadan

Getty ImagesHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
A Najeriya, mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III, wanda shi ne shugaban majalisar koli kan harkokin addinin musulunci ya bayyana ganin watan a garuruwa daban-daban a Najeriya a wani taron manema labarai da aka gudanar a daren Lahadi.
Wannan na zuwa ne bayan ganin jinjirin watan da aka yi a wurare daban-daban a fadin duniya
Kwamitin ganin wata na Najeriya ya wallafa jawabin sarkin a shafin Twitter inda sarkin ya umarci jama'a da su tashi da azumi ranar Litinin.
Akasarin Musulmai a fadin duniya za su tashi da Azumin watan Ramadan ranar shida ga watan Mayun 2019 wanda hakan ya zo dai-dai da daya ga watan Ramadan 1440.
Sarkin ya yi kira da a yawaita ibada a cikin watan na Ramadan kuma a ci gaba da addu'a ga shugabanni.
Baya ga Najeriya Musulmai a wasu kasashen duniya irin su Saudiyya za su fara azumin na watan Ramadana a ranar Litinin.
Ramadan dai wata ne mai alfarma ga musulmi inda ake matsa kaimi kan ibada da addu’o’i. 
Fatan Allah ya bamu ikon yin ibadojinmu cikin kwanciyar hankali da koshin lafia, ya kuma karbi ibadunmu. 

Comments

Popular posts from this blog

Is ‘Game of Thrones’ greatest TV show of all time?

Nigeria's Independence Day

Aubameyang, Salah da Mane sun lashe Kyautar Gwarzon Cin Kwallayen Premier