Auren Adam A. Zango

Adam A. Zango yana can yana cin angoncinsa tare da amaryar shi. Al’umma sun taya jarumin farin ciki da fatan alheri da shi da amaryar ta sa wato Safiya Umar Chalawa, wacce aka fi kira da Suffy.

An daura auren ne a masallacin fadar sarkin Gwandu da ke garin Gwandu, a jihar Kebbi. Majiyar mu ta sanar da mu cewar Zango ya yi aure sau biyar a baya, ya samu 'ya'ya shida; hudu maza, biyu mata, daga mat-a biyar da ya aura kafin su rabu.

Safi ko kuma Suffy kamar yadda ake kiranta, ita ce ta kasance matar Zango ta shida da ya aura. Majiyar mu ta ce Zango ya saki dukkan mata biyar da ya aura a baya, sai dai har yanzu ba ta san dalilin rabuwar sa da matan da ya ke aura ba.
A. Zango yayi aure na shida kenan a makon da ya wuce. Ga duka auren da yayi kamar haka:
1) Amina - dan su 1
2) Aisha - ‘ya’yanau 3
3) Maryam Nasarawa - dan su 1
4) Maryam A. B. Yola
5) Ummukhulsum - ‘yar su 1
6) Safiya Chalawa (Amarya)

Abin da mafi yawan mutane ke fada shi ne ba yin auren ba, rikon auren.

Mu dai daga nan fatan alheri mu ke wa jarumin da fatan Allah ya ba su zaman lafia, amin summa amin.

Comments

Popular posts from this blog

Is ‘Game of Thrones’ greatest TV show of all time?

Nigeria's Independence Day

Aubameyang, Salah da Mane sun lashe Kyautar Gwarzon Cin Kwallayen Premier